Matasan ‘yan mata Musulmi, sun bi sahun masu kare hakkokin mata a nan Washington, domin nuna juyayi kan kisan wata matashiya Musulma ‘yar shekaru 17 da aka yi yankin Sterling dake jihar Virginia a karshen makon da ya gabata.
A lokacin wani taro da aka shirya domin mutuwar matashiyar, wanda ya tattaro mutane daga bangarori daban-daban, mahalarta taron sun saurari addu’oi da wake da kuma jawabin karrama Nabra Hassanen daga limamai wadanda suka yi Allah wadai da kisan da hare-haren da ake kai wa mata da Musulmi da kuma bakaken fata ‘yan asalin Amurka.
Hukumomin sun ce Hassanen ta rasu ne bayan da ta samu mummunan rauni daga bugun da Darwin Martinez Torres mai shekaru 22 ya yi mata da kulkin wasan Baseball, a lokacin da ya kai musu hari tare da kawayenta.
Lamarin ya faru ne bayan da Hassanen da kawayenta, suka fito daga wani masallaci dake yankin Sterling domin neman abincin da za su yi sahur.
Kisan da aka yi wa matashiyar, ya harzuka jama’a da dama a nan Amurka, lamarin da ya sa mutane suka shiga shafukan sada zumunta suna kiran a gudanar da bincike.
Facebook Forum