Yayin da tattalin arzikin Najeriya ke tangal-tangal sanadiyyar faduwar darajar Naira, wanda hakan kuma ke da nasaba da faduwar farashin mai a kasuwannin Duniya, Shugabar Hukumar Lamuni Ta Duniya IMF, Christine Lagarde, za ta ziyarci Najeriya, inda za ta gana da Shugaba Muhammadu Buhari don tattauna batutuwa masu alaka da tattalin arzikin Najeriya da ma na kasa da kasa.
Haka kuma da masu ganin za a tabo batun kara rage darajar Naira a wannan ziyarar wuni hudu da gaggan jami’an IMF za su kai Najeriya daga wannan Talatar. Rahotanni na nuna cewa Lagarde za ta tattauna da jami’an Najeriya da Kamaru a daidai lokacin da kasashen ke fuskantar durkushewar tattalin arziki sanadiyyar dalilai iri-iri.
Wani masanin tattalin arziki da ke kasuwar canji Abuja mai suna Alhaji Hashimu Muhammad y ace wannan ziyarar ta na da tasirin gaske ganin yadda tattalin arzikin yankin ke rarrafe. To saidai ya bayyana fargabar yiwuwa tawagar ta IMF ta gabatar da wani sharadin da ba zai dadada ma ‘yan Najeriya ba.
Ga wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton: