ACCRA, GHANA - Bayan watanni biyu, tabarbarewar tattalin arzikin kasar na ci gaba da ta’azzara yayin da kudin Cedi ya zama kudi mafi karancin daraja a duniya cikin kwanaki uku da suka wuce, kamar yadda ma’aunin darajar kudi na Bloomberg ya nuna.
Duk da matakan da kwamitin, a karkashin jagorancin gwamna bankin Ghana, Ernest Addison ya dauka domin dakile faduwar darajar Cedi ba su haifar da mai ido ba.
Kamar yadda rahoton Bloomberg ya nuna, darajar Cedi ya fadi da kashi 3.3 cikin 100 a ranar litinin 17 ga watar Oktoba, 2022 inda canjin dalar Amurka ya kai cedi 11.3 a Accra. Rahoton yace, cedi ya fadi da kashi 45 cikin 100, mafi girma tsakanin kasashe 148. A yayin da ake hada wannan rahoton, dala ya kai cedi 12 a Accra.
Watanni biyu ke nan kasar na tattaunawa a hukumance da asusun lamuni na duniya (IMF), domin samun lamuni na dala biliyan 3 cikin shekaru uku. Asusun na IMF na tafiyar hawainiya wajen amincewa saboda yana bukatar tabbatar da tsarin dorewar biyan bashin.
Dalilan da Mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia ya bayar ga faduwar darajar Cedi, sun hada da magance matsalar tsarin bankuna da aka kashe kimanin dalar Amurka biliyan 7, da annobar coronavirus; da kuma yakin Rasha da Ukraine. Dalilan da masu fashin baki a kan harkokin kudi da tattalin arziki ba su amince da su ba.
Hamza Adam Attijjany, masani a kan tattalin arziki ya ce, bincike da asusun lamuni ta yin ya nuni cewa annobar coronavirus da yakin Ukraine da Rasha ba su ne dalilin faduwar darajar kudi da tattalin arzikin Ghana ba. Amma dalilai ne na cikin gida da bankin Ghana ta kasa magancewa.
Kamar yadda al’ummar gari ke kokawa, baya ga tsadar rayuwa, faduwar darajar kudin ya koma da sana’oinsu baya domin ko da yaushe canjin kudi na hawa ne.
A karshe Hamza Adam Attijjany ya nuna, duk matakan da gwamnati ta dauka na kara farfado da darajar cedi na kan hanya, amma gwamnati ta magance hauhawar tashin farashin kayayyaki ta hanyar bunkasa noma da inganta kayan da ake fita da su kasashen waje. Kuma gwamnati ta shiga yarjejeniya da kasashen waje da kudin Cedi ba kudin kasar waje ba.
Sannan kuma ta san kudaden da masu zuba hannun jari ke fita da su daga kasar tare da tabbatar da cewa sun fita ne da Cedi ba kudin kasar waje ba.
Ranar laraba, 19 ga watan Oktoba kungiyar masu saye da sayarwa na Ghana (GUTA) suka fara yajin aiki a birnin Accra, domin muntsinin gwamnati ta gaggauta magance matsalar faduwar darajar Cedi.
Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah Bako: