Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dapchi: Har Yanzu Babu Labarin Leah Sharibu


Shugaba Buhari ya gana da daliban makarantar Dapchi da aka dawo.
Shugaba Buhari ya gana da daliban makarantar Dapchi da aka dawo.

A ranar 19 ga watan Fabrairun wannan shekarar ne mayakan kungiyar Boko Haram suka afka garin Dapchi a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, suka sace 'yan mata fiye da 100. Ko da yake, sun dawo da 'yan matan bayan wata guda, amma har yanzu ba a saki wata daliba guda ba mai suna Leah Sharibu.

Bayanai daga Najeriya na cewa, har yanzu ba a jin duriyar daliba guda da ta rage mai suna Leah Sharibu, mai shekaru 15, wacce tana daga cikin daliban da aka sace a Dapchi.

Iyayen Leah Sharibu sun shiga wani hali na zullumi da fargaba game da halin da ‘yarsu ke ciki.

Mista Nathaniel Sharibu, mahaifin yarinyar ya fadawa Muryar Amurka cewa, har yanzu babu wani takamaiman batu akan yunkurin kubutar da ‘yarsa.

Shugaban kungiyar iyayen da aka sace ‘ya‘yansu na garin Dapchi, Bashir Alhaji Manzo, ya ce ya tuntubi gwamnatin jiha inda suka tabbatar masa kokarin da suke yi.

Haka kuma ba su zauna ba a kungiyance domin neman hanyar da za a bi don kubutar da Leah.

A kwanakin baya, hukumomin Najeriya sun ce, suna iya bakin kokarinsu wajen ganin an sako dalibar, inda har Sipeto Janar na 'yan sandan kasar, Ibrahim Idris, ya ce tana dab da komowa gida.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda Biu

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG