Yayinda yake bada kasida a jami'ar Legas, albarkacin tunawa da ranar samun 'yancin Najeriya, mataimakin shugaban kasar Indiya Farfasa Muhammad Hamid Ansari yace kasashen biyu Ingila ce tayi masu mulkin mallaka ta dalilin haka suna da dangantaka da zata sa su hada hannu su taimaka wurin habaka mulkin dimokradiya a nahiyoyinsu.
Yace Indiya ita ce kasar dimokradiya mafi girma a duniya kuma ta biyu mafi yawan jama'a a duniya haka ma Najeriya ce kasar dimokradiya mafi girma kuma mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka. Yace kasashen sunyi gwagwarmaya da mulkin mallaka ta Ingila. Idan kasashen biyu suka hada kai zasu fitar da wata duniya ta daban da zata nuna inda aka dosa a wannan karni da ake ciki.
Farfasa Ansari yace akwai bukatar yin anfani da matasan da Allah ya albarkaci kasashen biyu dasu domin cigabansu. Tun lokacin da Indiya ta samu 'yancin kai ta fitarwa kanta alkiblar da zata dosa a cewar mataimakin shugaban kasar Indiya. Yace alamarin yanzu ya fara kai kasarsa dagaci.
Ta dalilin haka yayi kira ga 'yan Najeriya da suyi koyi da kasarsa ta Indiya wajen mantawa da banbancen siyasa da kabilanci da kuma addini domin tunkarar cigaban al'umma da kuma kasa baki daya.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.