Tsohon Frayim Minista Seini Oumarou ya rugumi kaddara a zaben shugaban kasar jamahuriyar Nijer.
A jiya Laraba Oumarou Ya gayawa manema labarai cewa bai goyi bayan a bukaci kotun tsarin mulkin kasar Jamahuriyar Nijer ta soke sakamakon zaben ba. Ya ce ya yi hakan ne don kar ya jefa kasar Jamahuriyar Nijer cikin wahalhalun da ba su da iyaka.
Ranar Litinin da ta gabata hukumar zaben kasar (CENI) ta bada sakamakon cewa dadadden madugun 'yan hamayya Mahamadou Issoufou ne ya lashe zaben da kashi 58 cikin dari, shi kuwa Seini Oumarou ya samu kashi 42 cikin dari.
Matakin da Seini Oumarou ya dauka na rungumar kaddara ya share hanyar komawa ga mulkin farar hula ba wata gargada a kasar Jamahuriyar Nijer, bayan sojoji sun fi shekara daya su na mulkin kasar.
Idan ba a manta ba dai a cikin watan Fabarairun shekarar Dubu Biyu da Goma sojoji su ka hambare shugaba Mamadou Tandja daga mulki, bayan da ya tilasta yin wasu sauye-sauyen kundin tsarin mulki domin ya tsawaita wa'adin shi na mulki kuma ya karawa kan shi iko.