Jami’an zabe a Nijar sun bada labarin cewa an yi zaben fidda gwani na kasar cikin lumana ba tareda wani cikas ba. Ana sa ran samun sakamakon zabe cikin makon gobe.
Shugaban kasar Nijar Janar Salou Djibo yace Nijar tana iya zama abar koyi kan Demokuradiyya a nahiyar.
Ahalin yanzu kuma yau lahadi ce ake zaben shugaban kasa a kasar benin,ind a shugaba Boni Yayi yake neman wa’adi na biyu,a zabe d a ya fuskanci tsaiko har sau biyu,a dai dai lokacinda jama’a suke kara nuna rashin jin dadinsu a kasar.
An jinkirta zaben ne da nufin baiwa jami’ai damar yi wa jama’a rijista. Da an ayyana zaben ne cikin watan febwairu.
A Cadi kuma,dan hamayya dake takarar shugaban kasa, yace shugaba Idris Deby ya amince da bukatar su na dage zabe, kwana daya kamin a fara kaddamar da yakin neman zabe.
Naji Madou, ya gayawa manema labarai cewa, shugaban kasa Deby, ya gana da shi da wasu ‘yan takara hudu jiya Asabar.Ya ce dukkansu sun amince da tsara wani sabon jadawalin zabe, wanda tun farko aka ayyana yi ranar 3 ga watan gobe.
Madou yace ana sa ran bada snarwar sabon jadawalin ranar Talata idan Allah ya kaimu.