Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Ra'ayin Rikau, Kavanaugh Ya Zama Alkali a Kotun Kolin AMurka


Brett Kavanaugh
Brett Kavanaugh

Bayan an shafe makwanni ana zafafan muhawarori da takaddama da kuma zarge-zarge kan cancanta ko rashin cancantar Brett Kavanaugh a matsayin alkali a Kotun Kolin Amurka, daga karshe dai, jiya Asabar Majalisar Dattawan Amurka ta amince da nadin nasa.

Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da Brett Kavanaugh a matsayin alkali a kotun kolin Amurka, bayan an shafe makwanni ana tafka takadda kan zarge-zargen da ka masa na yunkurin yin fade, da halayyansa, da kuma zafin rai.

An amince da nadin alkali Kavanaugh a babban zauren Majalisar Dattawan Amurkar da kuri'u 50 akasin 48. Sanata Steve Daines mai wakiltar Montana bai samu zuwa ba, saboda ya na wurin bukin daurin auren diyarsa. Wannan ya sa Sanata Lisa Murkowski mai wakiltar Alaska, wadda ada ta yi niyyar kada kuri'ar rashin amincewa, ta canza kuri'arta daga ta rashin amincewar zuwa, abin da ake kira, "kuri'ar kasancewa," wanda wannan wani tsari ne mai hada kuri'ar Sanatan da ya yi niyyar kadawa amma bai samu zuwa ba, da kuri'ar Sanatan da ya ke zauren, amma bai amince ba, su kasance kuri'a guda ta amincewa, muddun Sanatocin biyu sun yadda.

Bayan kada kuri'ar amicewar, Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ta kadar twitter cewa ya yaba tare kuma da taya Majalisar Dattawan murnar amicewa da alkali Brett Kavanaugh, wanda ya kira "Shahararre."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG