Dan jam’iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Tarrayar Amurka mai wakiltar Georgia, John Lewis, na daya daga cikin sanannun ‘yan kasar da su ka shahara a bangaren kare hakkin dan a dam tun daga shekarar 1960.
To amma Lewis ya fadi jiya Laraba cewa zai kaurace ma kaddamar da Gidan Adana Kayan Tarihi na Mississippi da za a yi ranar Asabar muddun dai Shugaba Donald Trump zai hallara.
Lewis da wani dan jam’iyyar Democrat a Mississipi Bennie Thompson, sun rubuta takardar hadin gwiwa ta yin watsi da bukin bude gidan kayan tarihin a matsayin “cin fuska” ganin Trump ne zai kaddamar da shi.
“Kalaman Trump na kaskantar da mata da nakasassu da bakin haure da kuma ‘yan wasan kwallon kafar Amurka” cin mutunci ne ga wadanda su ka yi gwagwarmaya tare kuma da rasa rayukansu wajen neman adalci ga Bakaken fatan Amurka, a cewar takardar hadin gwiwar da su ka rubutan.
Wasu kuma bakaken fatan ‘yan siyasa sun ce za su kaurace ma bukin bude gidan kayan tarihin. Babbar kungiyar rajin kare hakkin dana dam ta kasar NAACP ta bayyana rawar da Trump ke takawa game da hakkin dan adam abin “takaici.”
Za a kaddamar da Ginin Kayan Tarihin ‘Yancin Dan Adam dinne gobe Asabar a birnin Jackson. Zai karfafa nazari kan irin jina-jinar da aka yi a gwagwarmayar na kare hakkin dan adam daga shekara ta 1945 zuwa 1976.
Abubuwan da za a baje a gidan sun hada da makaman gallazawa ta matukar tsana kamar alamar gicciye ta kungiyar Ku Klux Klan da kuma bindigar da aka kashe dan gwagwarmaya Medgar Evers.
Facebook Forum