Wonder ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da Oprah Winfrey inda ya fada mata dalilinsa na yanke wannan shawarar kamar yadda gidan talbijin na CNN ya nuna.
“Ina so na ga kasar nan ta dawo wuri mai annashuwa. Sannan ina bukatar na ga hakan kafin na koma Ghana, domin ba bu haufi zan yi hakan.” Wonder ya ce.
Da Winfrey ta tambaye shi ko zai koma zama a Ghanar a mataki na dindindin ne? sai ya ce, “e, haka ne.”
A cewar Wonder, “ba na so na ga tattaba-kunnena su na neman “dole sai an so su, ko su na magiyar sai an girmama su, ko su rika cusa ra’ayin nuna cewa su na da muhimmancin, wannan wane irin abu ne?”
Wonder na nuni ne da yadda matsalar nuna wariyar launin fata musamman akan bakaken fata ta yi kamari.
Mawaki Stevie wanda ya rera fitattun wakoki irinsu “Part Time Lover,” “You Are the Sunshine In My Life,” da “I Just Called To Say I love You.”
Ya lashe lambobin yabo na Grammy har sau 25 an kuma taba zabensa sau 75 don neman lambobin.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Wonder dan shekara 70 ya fara nuna sha’awarsa ta komawa Ghana ba, a shekarar 1994, ya taba yabawa da yanayin zamantakewar kasar “ta fuskar yadda al’umarta take hada kai,” fiye da Amurka.
Stevie Wonder dan asalin jihar Michigan ne, ya kuma tsunduma cikin harkar wake-wake ne tun yana dan shekara 9 inda a shekarar 1961, kamfanin waka na Motown ya kulla wata yarjejeniya da shi.