Mai horar da ‘yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya yi karin haske kan dalilan da yake ganin suka sa ‘yan wasan Madagascar suka lallasa Super Eagles a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Masar.
Yayin da yake amsa tambayoyi a hirar da shafin Twitter na kungiyar kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF ta yi da shi bayan an kammala wasan, Rohr ya ce, duk da cewa ‘yan wasan Najeriya ba su nuna bajintarsu ba, ya kamata a fahimii cewa tawagar ta Madagascar ta buga kwallon a zo-a-gani.
“Yan wasan na Madagascar, sun cancanci su lashe wannan wasa, saboda sune suka buga kwallo, mu ne muka fi rike kwallo amma babu kuzari a bangaren ‘yan wasanmu.” Inji Rohr.
Madagascar ta lallasa Najeriya da ci 2-0, wanda hakan ya zamanto karon farko da aka doke ta tun da aka fara gasar.
Tun dai gabanin karawar Najeriya da Guinea, tawagar ‘yan wasan take kokarin kauracewa wasan saboda ba a biya ta kudaden alawus-alawus din su ba.
Wasu masu fashin baki a fannin kwallon kafa na da ra'ayin cewa wannan batu ya taka rawa wajen rashin kuzarin da aka gani a bangaren Najeriya.
Yanzu Madagascar ce ke jagorantar rukunin B da maki 7 yayin da Najeriya ke biye da ita da maki 6.
Wasannin Da Za a Yi Yau
Afirka ta Kudu da Morocco
Namibia da Ivory Coast
Tanzania da Algeria
Kenya da Senegal