Harward ya fada a wata sanarwa cewa, “wannan aiki ne da ake bukatar mutum ba dare ba rana, kwanaki bakwai a cikin mako, da kuma cikakken mika kai domin tabbatar da gudanar da shi daidai yadda ya kamata.
"Yanzu haka ba zan iya irin wannan sadaukar da kan ba." In ji Harward.
Mai shekaru 60 da haihuwa, Harward wanda tsohon sojan kundubalar mayakan ruwa ne, ya na kuma magana da harshen Farsi radau.
Ya yi ritaya daga aikin soji a shekara ta 2013, yanzu haka kuma yana aiki a matsayin babban jami’I a kamfanin Lockheed Martin, kamfanin makamai da ayyukan jiragen sama mai kula da harkokin hamfanin inda yake maida hankali kan jiragen United Arab Emirate.
Facebook Forum