Bayanai na ci gaba da bayyana kan dalilin da ya sa Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sallami kwamishinan ayyuka da samar da ababan more rayuwa, Eng. Mu’azu Magaji.
An sallami Magaji ne saboda wasu kalamai marasa dadi da ya yi game da rasuwar tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Mallam Abba Kyari wanda ya rasu a ranar Juma’a.
“Mai girma @GovUmarGanduje ya sallami kwamishinan ayyuka da samar da ababan more rayuwa, Engr. Mu’azu Magaji, bayan da ya yi wasu kalamai da ba su dace ba kan marigayi shugaban ma’aikatan fadar gwamantin tarayya Malam Abba Kyari.” In ji Salihu Yakasai wani hadimin gwamna Ganduje, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter @Dawisu.
Kyari ya rasu ne bayan fama da cutar coronavirus bayan da ya dawo daga kasar Jamus a karshen watan Maris.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar ta kara da cewa, “a matsayinsa na mai wakiltar al’uma, ya kamata a ce ya kiyaye duk wasu kalamai da za su kaskankantar da mukaminsa.”
“Duk wani ra’ayi na gashin-kai ko akasin haka da wani mai rike da mukamin gwamnati ya nuna, zai iya yin tasiri akan gwamnatin.” In ji sanarwar ta Garba.
Sai dai duka jami’an gwamnatin biyu na Kano ba su ambaci takamaiman abin da kwamishinan ya fada ba, amma rahotanni da dama sun ce a shafinsa na Facebook ya wallafa bayanan.
Amma jaridar Daily Nigerian ta yanar gizo, ta ruwaito cewa, kwamishina Magaji ya nuna farin cikinsa da mutuwar Kyari, inda ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “yanzu Najeriya za ta samu sarari,” kamar yadda jaridar ta ruwaito.
Facebook Forum