Ofishin uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ya ba ma’aikatansa hutun da sai baba ta gani yayin da ake shirye-shiryen bukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Wata sanarwa da ofishin mai dakin shugaban kasar ta fitar a ranar Talata dauke da sa hannu mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin lafiya da abokanan hulda ta ci gaba, Dr Mohammed Kamal ta ce an kulle ofishin ne saboda bukukuwan da ke tafe.
“A dalilin haka, muna umartar dukkan ma;aikata da su tafi hutu har sai an neme su.” Sanarwar wacce aka wallafa a shafin Twitter na uwargidan shugaban kasar ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa ma’aikatan “za su iya yin ayyuka daga gida idan hakan ta kama kamar yadda aka yi a baya.”
Ofishin uwargidan shugaban ya kuma mika godiyarsa ga ma’aikatan saboda irin jajircewa da suke yi wajen gudanar da ayyukansu.
Bisa al’ada akan ba ma’aikatan fadar shugaban kasa da na gwamnati hutu a lokacin bukukuwa makamantan wadanda ke tafe amma ba kasafai ake ba su umarnin su zauna a gida har sai an neme su ba.
Wannan mataki da ofishin Aisha Buhari ya dauka na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da ta dawo daga kasar Turkiyya tare da shugaba Buhari.