Uwar gidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta ba Ma’aikatar harkokin mata da asibitin gwamnatin tarayya dake Abuja tallafin kayan abinci da kayan asibiti, ciki har da magunguna a matsayin gudummowar ta a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar coronavirus, a cewar wata sanarwa da aka turawa manema labarai. Babbar mai taimaka wa Shugaban kasa a harkokin mata, Dr. Hajjo Sani ce ta gabatar da kayayyakin ranar Laraba 29 ga watan Afrilu a madadin matar Shugaban.
Kayayyakin asibitin sun hada da tarin man tsaftace hannu mai kashe kwayoyin cuta, kayan kariya da suka hada da rigar kariya, takunkumin rufe hanci da baki da kuma safar hannu.
Ministar Ma’aikatar mata, Dame Pauline Tallen ce ta karbi kayayyakin yayin da shi kuma babban darakta Farfesa Sa’ad Ahmed ya wakilci asibitin gwamnatin tarayya. Manyam jami’an sun yaba da tallafin da matar Shugaban ta bayar sun kuma yi alkawarin zasu raba kayayyakin ga wadanda aka bada dominsu.
A gefe guda kuma, Hajiya Aisha Buhari ta danka wa Ministar kayan abinci don a raba wa mata da kungiyoyin mata a matsayin tallafi a daidai lokacin da ake zaman kulle sakamakon cutar coronavirus. Kayan abincin sun hada da bahunan shinkafa, gero, sukari, galan-galan din mai da kuma tumatirin gongoni.
Facebook Forum