Jami'ai a babban birnin Florida sun shirya a yau Laraba domin daruruwan dalibai da za su yi tattaki domin kira ga wakilan majalisar dokokin jihar, su zartas da kuduri da zai takaita ko tsaurara mallakar bindiga.
Wannan na zuwa ne bayan mummunan harin kan mai uwa da wabi a wata makarantar sakandare a kudancin jihar.
Dan bindiga ya harbe mutane 17 a makarantar sakandare mai suna Marjory Stoneman Douglas dake Parkland a satin da ya gabata. Dalibai daga makarantar da kuma wasu daga wasu wurare a Florida da sauran jihohi suka tashi haikan don ganin shugabanni a matakin jiha da na tarayya sun dauki matakin hana haka sake aukuwa.
Fiye da daliban Stoneman Douglas 100 ne suka shiga motoci zuwa birnin na Tallahassee don su shiga gangami dajerin gwanon a yau Laraba, haka nan zasu gana da shugabannin majalisar dokokin jahar.
Gami da kari bayan gangamin na yau laraba a Talahassee, Shugaba Donald Trump, bayan shawarar da ya bayar na haramta na'urorin da ka iya maida bindigogi zuwa makamai masu sarrafa kan su, da kuma karfafa bincike akan masu sayan bindigogi, Shugaban na Amurka Donald Trump zai jagoranci zaman sauraro a yau Laraba a fadar White House da dalibai, da Iyaye gami da malamai wadanda harbin kan mai uwa da wabi ya shafa a Amurka.
Facebook Forum