Ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Bornon Najeriya da ke arewa maso gabashi, ta aikawa shugabar kwalejin koyon aikin jinya Rukaiya Shettima Mustapha wasikar tuhuma bisa zargin dakatar da wasu dalibai da ta yi daga zuwa makaranta, saboda sun ki zuwa tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Buhari ya kai ziyara jihar ta Borno a ranar 17 ga watan Yunin inda ya je ya kaddamar da wasu ayyuka tare da duba yanayin tsaro a jihar wacce ke fama da matsalar Boko Haram.
Wasu rahotanni sun ce shugabar kwalejin, ta dakatar da wasu dalibanta saboda sun ki zuwa tarbar Shugaba Buhari, abin da gwamnatin jihar ta Borno ta ce azarbabi ne.
“Mun ba ki sa’a 48 ki aiko mana da amsa kan dalilin da zai sa ba za a dauki mataki akan ki ba.” Kwamishinar lafiya a jihar Juliana Bitrus ta ce cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a karshen mako.
Lambar wasikar da aka aikwa shugabar kwalejin ita ce MOH/PER/752 V.1.
“Duk da cewa an saba sa dalibai su tarbi shugabannin kasa a duk fadin Najeriya, ana bari su yi ne bisa ra’ayin kansu.
“Ma’aikatar lafiya ta yi matukar mamaki, da muka ji labarin shugabar ta dauki wannan mataki. Mun kuma kwashe lokaci muna bincike kafin mu aika mata da wannan wasikar tuhuma.” In ji Bitrus.
Kwamsihiniyar lafiyar ta kara da cewa, akwai yiwuwar shugabar kwalejin, ta yi amfani ne da zuwan Buharin ne don ta hukunta daliban saboda wani dalili na daban.
A cewar Bitrus, shugabar kwalejin, ta yi hakan ne kawai don ta janyo batanci ga gwamnatin jihar Borno, “abin da ya kaita har ta ba daliban wasiku dauke da sa hannu.”
“Saboda haka, wannan mataki da ta dauka, ta yi shi ne bisa radin kanta ba tare da wani magabacinta ko jami’in gwamnati ya sa ta ba.” In Kwamsinar lafiyar.
A ranar Juma’ar da ta gabata rahotanni suka ruwaito Shugabar kwalejin Rukaiya ta ba dalibai akalla 30 wasikar dakatarwa daga zuwa makaranta saboda sun ki bin umarnin da aka ba su na zuwa yin maraba ga Shugaba Buhari.