Ta hanyar wata takarda da aka aika a ranar alhamis din da ta gabata ne hukumomi suka sanar da Dr. Dille Ismouha cewa sun dakatar da aikin kwantagarin da ta ke yiwa sashen kula da masu cutar daji a asibitin birnin Yamai.
Raba hankali tsakanin asibitin gwamnati da kungiyar SOS Cancer wacce Dr. Dille Ismouha ke shugabanta ita ce hujjar da aka bayar wajen dakatar da ita daga wannan asibiti, sai dai a cewar ta tonon asirin da ta yi game da kudaden fitar da marassa lafiya zuwa kasashen waje ne ke mafarin wannan mataki.
Bangaren gwamnati dai bai ce uffan ba game da batun ya zuwa yanzu a yayinda kungiyar kwararrun likitoci a na ta bangaren ke gudanar da wani taro don duba ta inda za ta bullowa wannan sabon al’amari da ke ci gaba da jan hankali.
A watan da ya gabata ne Dr. Dille Ismouha, a hirar ta da wata tashar telebijin mai zaman kanta ta bayyana damuwa akan yadda wasu jami’ai a ma’aikatar kiwon lafiya ke fakewa da tsarin aika masu fama da cutar cancer zuwa waje don fitar da makudan kudade daga aljihun gwamnnati.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum