Da yake jawabi wajen yaye wasu zaratan sojojin Sama na musamman da Rundunar sojin Birtaniya ta horas, Babban Hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, ya ce za su ci gaba da ragargaza yan ta'adda.
An dai horas da sojojin ne a fannin samar da tsaro ga abokan aikinsu sojoji tare da nemo da kuma ceto wadanda suka shiga wani irin yanayi yayin fafatawa.
Babban Hafsan sojin saman ya ce wannan horo, zai bai wa mayakan damar sanin makama yayin da suke fafatawa su kadai ko da sauran abokan aikinsu cikin kowane irin yanayi.
Cikin jawabinsa, kwamandan horaswar, Wing Commande Steven Senkegor ya ce yadda salon yaki ke canzawa, su ma sun canza salon horin da suke ba da horon.
Ya ce ana ba su horon ne ta yadda za a kimtsa mayakan wajen tunkarar duk wani matsalar ko ta kwana, sannan su fafata duk cikin yanayin da suka sami kansu a sama, ko ruwa ko a kasa.
Wani masanin Tsaro, Wing commander Mia Isa Salmanu da ya taba da yadda ake ba da wannan horo ya ce lalle hakan zai taimaka wajen sake sanya dakarun cikin shiri.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Kaduna:
Facebook Forum