Dakarun kasar Habasha na samun nasara a garuruwa da yawa a kusa da babban birnin yankin Tigray, kwana daya bayan da gwamnatin kasar ta ce ta fara kaddamar da matakin karshe na farmakin da ta ke kaiwa a yankin da ke arewacin kasar, a cewar kafar yada labaran Habasha ranar Juma’a 27 ga watan Nuwamba.
Laftanal Janar Hassan Ibrahim ya fada a wata sanarwa a ranar Juma’a cewa dakarun gwamnatin tarayya sun kwace Wikro kuma zasu mallake Mekelle nan da ‘yan kwanaki, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.
Ba a samu wata kafa mai zaman kanta dai da ta tabbatar da ikirarin gwamnatin ba. An yanke hanyoyin sadarwar waya da na yanar gizo a yankin tun a lokacin da sojojin gwamnatin Habasha suka fara kai farmaki a farkon watan nan na Nuwamba.
Ci gaba da fadan na faruwa ne bayan da Firai ministan Habasha Abiy Ahmed, biyo bayan ganawa da wakilan kungiyar hadin kan Afrika ta AU, ya sake nuna cewa babu batun zaman shawarwarin sulhu da shugabannin yankin Tigray.