Gobe Alhamis ake sa ran za a bude sabon filin saukar jiragen sama da aka dade ana jira a Dakar babban birnin kasar Senegal.
An kammala dukkan ayyukan da suka kamata a wannan sabon filin jirgin sama mai suna Blaise Diagne, a bayan da aka kwashe sama da shekaru goma ana aikinsa.
Filin jiragen mai nisan kilomita 47, daga Dakar babban birnin kasar, ya hade da babbar hanyar zirga zirga ta kasar Senegal, kuma za a hade shi da tashar jirgin kasa da ake sa ran zata fara aiki a shekarar 2019.
Wannan sabon tsari na daga cikin shirin rage cunkoson jama’a a birnin da kuma mayar da Senegal cikin manyan biranen yammacin Afirka.
Facebook Forum