Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dagumawa: Matasa Na Bukatar Sanin Tarihin Najeriya Kafin Su Iya Tafiyar Da Kasar


Injiniya Rufa'i Dagumawa
Injiniya Rufa'i Dagumawa

Shirin mu na matasa da siyasa na wannan mako ya samu bakuncin Injiniya Rufa’I Dagumawa wakili a kungiyar Arewa Youth Assembly Gammayar, kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya.

Injiniya Rufa'i yace lokaci yayi da matasa zasu gano cewa dole sai sun san tarihin kasar, da hanyoyin magance matsalolinta, tare da sanin cewar dole sai matasa da dattijai sun hada kai kafin tafiyar da Najeriya.

Matashin ya bayyanawa wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, cewa duk kasar da take son ci gaba sai tayi amfani da matasa domin samun cigabanta.

Ya kuma ce a yayin neman zabe ana tafiya da matasa wajen yakin neman zabe, amma da zarar an kafa gwamnati sai a manta da su, don haka ya zama wajibi ga matasan su nazarci tarihin kasar nan, tun daga farkon samun 'yanci, da sanin yadda take tafiyar da siyasarta.

Ya kara da cewa mafi yawan matasan yanzu basu da tarihin yadda shugabannin baya suka mulki Najeriya, ya jaddada cewa ya zama wajibi matasa su san siyasar farko, da ta yanzu, su bibiyi yadda aka tafiyar da ita.

Kwamared Rufa’I ya ce dole ne matasa da dattijai su tafi hannu, da hannu kafin cimma bori.

A yanzu matasa suna da ilimin fasahar zamani, yayinda dattijai ke da basira da fikira na tarihin matsaloli, da hanyoyin samar da cigaban Najeriya. Domin haka sai an fuskanci juna ne za’a samu maslaha.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:29 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG