Gwamnatin jihar Legas ta ce zata kame duk wadanda suke da hannu cikin gina duk wani gini da ya rushe ko yayin da ake gina shi ko kuma bayan an kammala aikinsa. Gwamnan jihar Mr Babatunde Fashola ya ce kama daga injiniyoyin ginin da wadanda suka yi taswirin ginin da sabiyo-sabiyo da ma sauransu duk za'a kama su a hukuntasu.
Gwamnan ya karbi rahoto na musamman kan musabbabin rushewar gine-gine a Legas.Yayin da yake karbar rahoton kwamitin da ya kafa a karkashin Madam Abimbola Ajayi, gwamnan ya ce yana son ya jawo hankalin duk kwararru a jihar cewa idan gini ya zube kasa wata hujja zasu bayar cewa sun yi duk abun da ya kamata su yi wurin yin ginin. Ya ce ina takardun cewa su kwararru ne? Ya ce kwarewarsu nada alamar tambaya. Ya ce babu wata hujja da zata hana a kamasu a kuma hukumtasu.
Yayin da Madam Abimbola take mika rahotonta ta ce tsakanin shekarar 2007 kawo wannan shekarar gine-gine 130 suka rushe. Lokacin da suke gudanar da bincikensu ma gine-gine uku suka kara rushewa. Ta ce akwai bukatar daukan matakan gaggawa domin a kawo karshen rushewar gine- gine a jihar. Ta ce sun zabi gine-gine goma da suka rushe suka kai ziyara kana suka binciki musabbabin dalilan da suka sa suka rushe. Idan ba gwamnati ta tashi tsaye ta hukunta duk wadanda suka karya dokar gini a jihar ba, to lamarin ba zai canza kamanni ba.
Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.