Bayan sun sace shi sai suka wuce da shi Kano inda ya kwashe watanni tara tare da su a tsare. Daga Kano suka sake yin arangaba da shi zuwa Zaria inda a nan ma ya yi wata biyu kafin Ubangiji Ya yi masa gyadar dogo.
Mutumin mai suna Francis Colon ya samu ya arce ne lokacin da wadanda suke tsare da shi suka shiga yin sallah. Ko da ya fice sai ya tsayar da babur da ya kaishi ofishin 'yansanda mafi kusa. Daga can ne aka mika shi ga hekwatar 'yansandan dake Kaduna.
Kawo yanzu babu wanda ya san abun da 'yanbindigar suka nema awurinsa ko kuma irin aikin da ya zo yi a Najeriya har ya zauna garin Rimi cikin jihar Katsina. Binciken 'yansanda ne zai bada bayani.
Ga karin bayani.