Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, yayi kira da babbar murya da cewar, alkalai su taimaka mishi wajen yaki da cin haci da rashawa a kasar. A lokacin taron bita na lauyoyin kasar, da aka dudanar a garin Kaduna yayi wannan kiran. Yace idan bai samu hadin gwiwar lauyoyin kasar ba, to babu shakka yakar cin hanci da rashawa abune mai wahala ga gwamnatin shi.
Dalili kuwa shine, su lauyoyin suna zaman kansu ne, sai sun gabatar da aikin su yadda ya kamata, su cire son rai da bayyanar da gaskiya a kowane hali. Wasu lauyoyi a kasar suna ganin cewar wannan kiran yazo a dai-dai lokacin da ya kamata. Barista Modibbo Bakari, wani lauya ne mai zaman kanshi a Abuja, wanda yake ganin cewar ai shugaban kasa, ba da su yake magana ba, yana magana ne da masu bashi shawara a harkar shari’a. Ya kara da cewar lallai su a matsayin sun a lauyoyi masu zaman kansu, kokarin su shine, su kare duk wani wanda suke wakilta a ko ina don kwato mishi hakkin shi.
Kuma ya naso shugaban kasar ya sani, cewar babu wani alkali da ya zamana baragurbin alkali, da baya karbar abun goro batare da hada kai da lauyoyi ba. A wasu lokutta ma alkalai kan kai shari’a kotu, dan wani lauya da yake son suyi kashe muraba a tsakanin alkalin da lauyan. Domin kuwa alkalai su kanyi amfani da lauyoyi wajen karbar musu abun goro a wajen mutane. Hakan na nuni da cewar ya kamata kowa ya tashi tsaye, wajen ganin an yaki cin hanci da rashawa baki daya.
Sauran al’umah na kasar na ganin cewar babu yadda za’ayi a magance matsalar cin hanci da rashawa a kasar, idan har ba’a gyara zukatan lauyoyi da alkalai ba, domin kuwa sau da yawa, sun san cewar wannan mutumin da ake tuhuma yana da laifin, amma saboda wani abu da zai basu sai su kokarta wajen kare shi. Hakan gaskiya ba karamin koma baya bane, ga wannan yakin na shugaba Muhammadu Buhari, wajen yaki da cin hanci da rashawa ba. Sai suma mutanen Najeriya, ya kamata su kokarta wajen gyara zukatan su da yima kawunan su da sauran al’umah adalci, ta haka ne kawai za’a iya magance wannan mastalar gaba gadi.