Hukumar kuma ta nuna farin cikin rashin zamewar alhazan da suke amfani da kamfanoni su shiga Saudiya su zama 'yan takari.
Bayanan sun fito ne daga shugaban hukumar alhazan Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad a taro na musamman da kamfanonin da zasu dauki alhazan jirgin yawo su 150 kuma fiye da kamfanoni 200 da zasu kula da 'yan umura.
Hukumar tana hukumta kamfanonin bisa ga nauyin laifin da suka aikata. Wasu ma idan ta kama su dakatar dasu gaba daya suna yin hakan. Kowa ana yi masa hukumci daidai gwagwadon abun da ya aikata.
Domin gudunfadawa hannun dillalan bogi ko 'yan damfara ga maniyatta mataimakin shugaban kamfanonin hajji Aminu Agowa ya bada shawara da yin gargadi.Wajibi ne duk alhaji ya tabbatar kamfanin da zai yi anfani dashi yana da lasisin hukumar alhazai. Abu na biyu kowane kamfani ke da lasisi dole ne ya rataya hoton lasisin a ofishinsa.
Saudiya ta warewa Najeriya kujeru 76,000 domin aikin hajji.
Ga karin bayani.