An taba irin wannan yunkuri a zamanin gwamnati shugaba Goodluck Jonathan har kowa ya sa rai za'a sako 'yan matan amma bisa ga wasu dalilai da har gobe kasar bata sani ba sai yunkurin ya wargaje.
Ganin bidiyon da wani bangaren Boko Haram ya fitar tare da wasu cikin 'yan matan har ma da sa daya daga cikinsu tana kiran gwamnati ta dauki duk matakan da suka dace domin a sakosu, ya tada kaimin masu ruwa da tsaki ta wannan bangaren.
Shugabar kungiyar hana kangarewar matasa Halima Baba Ahmed na ganin za'a samu nasarar fitar da matan ta wannan hanya. Tace Boko Haram tayi hakan ne domin da an taba yin hakan amma haka bai cimma ruwa ba ya sa take son wata kungiya ta shigo tsakaninta da gwamnati. Idan har an samu kungiyar da ta shiga tsakani za'a ci nasara.
To saidai wani masanin harkokin tsaro Dr.Muhammad Bello na jami'ar Jigawa yace bin wannan hanya ba mai bullewa ba ce. Yace a duk duniya wa zai fito yace zai taimakawa wani dan ta'ada. Yace kasashe kamar su Amurka, Birtaniya, Faransa da makamantansu basa yi. Yace duk wadanda suke fitowa suna cewa sun sansu karye su keyi.
Dr. Bello yace 'yan Boko Haram ba 'ya'yan goyo ba ne. Mayaudara ne, su yaudari mutane, su yaudari gwamnati kana su cigaba da ta'asa. Yace an sha yi dasu amma babu abun da aka samu.
Akan a yi musayar firsinoni domin 'yan ta'adan su sako 'yan matan Chibok, Dr Bello yace an san wadanda ake tsare dasu amma babu wanda ya san wadanda suke yaki a daji. Idan ba'a yi hattara ba wani kuskure za'a sake tafkawa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani