Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Da Alamar a Kasuwar Wuhan ta China Cutar Corona ta Samo Asali"


Kwayar cutar corona
Kwayar cutar corona

Wani kwararre kan cututtukan da aka samu daga abinci da dabbobi wanda ke aiki da Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), jiya Jumma’a ya ce shi dai ya yi imanin cewa wata kasuwar da ke birnin Wuhan na kasar China inda ake sayar da dabbobi masu rai ta taka rawa sosai game da bullar cutar coronavirus wacce ke haddasa cutar COVID-19, to amma ana bukatar karin bincike don tabbatar da ainihin yadda abin da ya faru.

Gwamnatin China dai ta rufe kasuwar a watan Janairu a matsayin wani bangare na kokarin tsai da yaduwar cutar tare kuma da tsai da sana’ar saye da sayarwa da kuma cin namun daji.

Da ya ke magana da manema labarai a birnin Geneva, kwararre a bangaren cututtukan da ake daukawa daga abinci da dabbobin, wanda ke aiki da WHO, Peter Ben Embarek ya ce akasari wannan kasuwar na samar da nama da abin zaman gari ga miliyoyin mutane a duniya don haka a maimakon hukumomi su tsai da irin wadannan kasuwanni, ya kamata ne a bubbude.

Ya ce har yanzu ba a san yadda aka yi dabbobi masu rai ko kuma masu hada hada a kasuwar su ka kai cutar kasuwar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG