Shugaban Amurka Donald Trump bisa dukkan alamu a shirye ya ke ya yi watsi da shawarwarin da manyan hafoshin mayakan Amurka suke bashi, yayinda gwamnatinsa take ci gaba da tunanin hanyar da ta fi dacewa ta tunkarar Iran.
Trump yana fuskantar wa'adin ya sake sabunta yarjejeniyar da Amurka da wasu kasashen duniya suka kulla da Iran. Jiya Talata shugaban ya nuna cewa bashi da fargabar ya janye Amurka daga yarjejeniyar, idan sauran kasashe da aka kulla yarjejeniyar da su basu amince a gudanar da sauye sauye kan yarjejeniyar ba.
"Abububawa marasa kyau suna faruwa a Iran, shugaban na Amurka ya fada, yayin da yake karbar bakuncin Yerima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda ya kai masa ziyara a fadar White House jiya Talata.
"Batun sabunta yarjejeniyar zai taso wata mai zuwa, zaka ga abunda zai faru," shugaban na Amurka ya fada.
Facebook Forum