Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Lassa: Jihar Ondo Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutum Tara

Avro 2020 futbol çempionatının 16-cı turu
Avro 2020 futbol çempionatının 16-cı turu

Yayin da ake ci gaba da kokarin dakile yaduwar cutar zazzabin cutar Lassa da ke bayyana a wasu jihohin Najeriya, an tabbatar da mutuwar mutum tara a jihar Ondo wadanda suka mutu sanadiyar wannan cuta.

Hukumomi a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya, sun tabbatar da mutuwar mutum tara bayan da suka kamu da cutar zazzabin cutar Lassa.

Akalla mutane 102 hukumomin jihar suka tabbatar sun kamu da wannan cuta a kananan hukumomi takwas daga kananan hukumomi 18 da jihar ke da su.

“Sakamakon binciken da aka gudanar a dakin bincike, ya tabbatar da mutuwar mutum tara.” Inji gwamna Oluwarotimi Odunayo Ekeredolu, yayin wani taro a garin Owo.

Jami’an lafiya da gwamnan jihar sun yi kira ga jama’a da su yi sauri su garzaya zuwa asibiti mafi kusa idan suka fara jin alamun zazzabi.

Ita dai cutar zazzabin Lassa, ta kan samo asali ne daga beraye.

Wannan kuma ba shi ne karon farko da ta halaka mutane a Najeriya ba.

Saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG