Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Za a Iya Samun Karancin Kayayakin Kariya


Wani dan kasar Zambia lokacin da ya zo siyan magani a wani shago.
Wani dan kasar Zambia lokacin da ya zo siyan magani a wani shago.

Yayin da cutar Coronavirus ko kuma Covid-19 ke ci gaba da yaduwa, hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar karancin kayayakin kariya daga cutar, da kuma hauhawar farashinsu.

Ta kuma umarci kamfanoni da kuma gwamnatoci da su kara samar da kayayakin da kashi 40 yayin da mutane ke ta kara mutuwa sakamakon cutar.

A yanzu dai cutar na ci gaba da yaduwa a kasashen Koriya ta kudu, da Japan da Iran da Amurka da kuma nahiyar turai da dai sauransu.

Wasu kasashe da dama kuma, sun bayyana samun mutum na farko da ke dauke da cutar a kasashensu.

A yanzu a kalla kasashe 80 ne ke fama da wannan cutar ta Coronavirus.

A kasar Iran, wato kasa ta biyu wacce aka fi samun mace-macen masu dauke da cutar, likitoci na fama da karancin kayayakin aiki yayin da mutum 77 suka rasa rayukansu.

Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayyana rufe makarantu na tsawon makonni hudu.

A cewar WHO, tun bayan da aka samu bullar wannan cutar ake fuskantar tsadar kayayaki da dama musamman abubuwan rufe hanci da kuma irin rigunan da likitocin fida ke sawa.

Wannan cuta dai, wacce ta faro a cikin birnin Wuhan na China a karshen shekarar da ta gabata, na ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya.

A yanzu, yawan masu kamuwa da cutar ya haura masu dauke da ita a ainihin inda cutar ta bulla wato China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG