A daidai lokacin da hukumar kare hakkin bil'adama ke gargadi ga jami’an tsaro akan su san yadda zasu gudanar da ayyukansu a yayin da ake aiwatar da dokar hana fita ba tare da kwakkwaran dalili ba a wasu jihohin Najeriya don yaki da yaduwar kwayar cutar coronavirus da akewa lakabi da COVID-19, yanzu an fara samun takun saka a tsakanin jami’an tsaro da kuma 'yan jarida.
A baya bayan nan wani baturen 'yan sanda wato DPO, ya jagoranci wasu 'yan sanda cikin motoci uku, zuwa cibiyar 'yan jaridu dake birnin Yola a jihar Adamawa, ba tare da saurara wa shugabanin 'yan jarida ba, suka kama wasu 'yan jaridar dake aiki a wurin.
Mallam Abdullahi Tukur, wakilin gidan rediyon Najeriya Kaduna kuma shugaban kungiyar wakilan kafofin yada labarai a jihar, ya bayyana takaicinsa game da abin da ya faru.
To sai dai kuma, rundunar 'yan sandan jihar Adamawa a ta bakin kakakinta DSP Suleiman Yahya Nguroje, ta musanta zargin cin zarafin 'yan jaridar.
Wannan na zuwa ne, yayin da hukumar kare hakkin bil'adama da ake kira National Human Rights Commission, da kuma wasu kungiyoyin fafutika ke hada hancin alkalumman koke-koke da kuma wuce gona da irin da ake zargin jami’an tsaro na yi a wannan lokaci na takaita zirga-zirga da gwamnati ta yi.
Kwamared Gambo Daud, na cikin 'yan rajin kare hakkin bil'adama a Najeriya, ya bayyana matakan da kungiyarsu ta dauka game da abun dake faruwa. Ya ce duba da rahotanin koke-koken da ake samu na cin zarafin jami'an tsaro ya sa suka tura wakilansu don su tattaro masu bayanan abubuwan dake faruwa.
Saurari cikakken bayani cikin sauti.