Miliyoyin mutane a duk fadin duniya na shagulgulan ranar Good Friday, ranar da mabiya addinin Kirista suka yi imanin cewa an giciye Annabi Isah Almasihu a birnin Kudus.
Ayyukan ibada na bana sun banbanta da yadda aka saba yi a ko da yaushe, yayin da mafi akasarin masu ibada suke kallon addu’o’in ta kafafen watsa labarai, a maimakon dammar taruwa a majami’u, a daidai sa’adda duniya ke fama da annobar COVID-19.
Mafi akasarin al’ummar duniya na cikin gidajen su domin kaucewa yaduwar mummunar cutar mai kisa.
A cewar cibiyar nazarin cutar ta Jami’ar John Hopkins fiye da mutum miliyan 1 da dubu 600 suka kamu da cutar.
Amurka ita ce matattarar cutar a yanzu da take da mutane sama da 466,000 da suka kamu da cutar.
Kasar Girka Spain ita ce ta biyu da mutum 153,222 sai Itaiya da take da mutum 143,626.
“Annobar ta haddasa babban kalubale ga zaman lafiyar kasa-da-kasa, da tsaro. Hasali ma ta kara yawan rashin tabbas a harkokin yau da kullum, da tashe-tashen hankali, da zasu karya mana lagon kokarin yaki da cutar”, a cewar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniiya Antonio Guterres, a rubutaccen jawabinsa lokacin wani taron sirri na majalisar tsaro ta hukumar.
Shugaban Amuka kuwa Donald Trump a lokacin wata ganawa akan annobar a jiya Alhamis, da alama ba ya tunanin akwai bukatar yin gwaji na gama garin mutanen kasar, duk da cewar akasarin masu dauke da wannan cutar sun bayyana alamun ta a fili. “A nan fa ana maganar mutun sama da miliyan 325 ne fa, wannan ba zai yuwuwa ba, idan kuka duba, hakan ba zai taba samuwa ba.” Wasu kasashen sun yi, amma sun yi don basu da yawa ne.
Facebook Forum