Wani bincike da masana a Amurka su ka gudanar na nuni da cewa cutar nan mai kisa ta coronavirus da ta fara bulla a tsakiyar kasar China, ta fara yaduwa ne tun kafin a bayyanawa duniya.
A cewar masana kimiya daga cibiyar lafiya ta jami’ar Harvard da Jami’ar Boston da asibitin yara ta Boston, bayanai da aka samu ta na'urar tauraron dan adam sun bayyana cewa an samu cunkoson motoci a asibitoci a birnin Wuhan tun a watan Agustan bara.
Wannan ya dada karuwa a watan Disamba lokacin da Beijing ta fara ankarar da hukumar lafiya ta duniya WHO game da sabuwar cutar da aka yi mata lakabi da COVID-19.
Hotuna sun nuna daya daga cikin asibitocin da aka bincika, Tianyou, an ga abun hawa 285 a wajen ajiyar motoci cikin watan Octoban 2019, wanda ya nuna karuwa da kashi 67 cikin dari idan aka kwatanta da 2018 inda aka ga abun hawa 171 kawai.
Binciken ya kuma nuna karuwar zuwa asibiti da kuma bincike ta hanyar amfani da kafar bicike ta China, Baidu ta yanar gizo don neman bayani kan ‘tari’ da ‘gudawa.’
Ana da yakinin cewa cutar coronavirus ta faro ne daga wata kasuwa a Wuhan a disambar 2019.
Masu binciken sun ce duk da yake ba su tabbatar karuwar zuwa asibitin na da alaka da COVID-19 ba, amma ‘shaidar da su ka samu ta goyi bayan wadansu shaidu da suka nuna cewa, cutar ta bulla kafin a tabbatar da ita a kasuwar kayan abinci ta dangin kifi."
Facebook Forum