Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta nemi Majalisar Dokokin kasar ta amince da kafa wata gidauniya ta naira biliyan 500 domin tunkarar cutar COVID-19.
Ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan bayan wani zama da suka yi da shugabannin majalisar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Ministar ta ce za a nemi kudaden ne daga asusu-asusun gwamnatin tarayya na musamman, basussukan da kudaden tallafin da ake san ran samu daga hannun kamfanoni ko kungiyoyi.
Jaridar yanar gizo ta Premium Times ita ma ta ruwaito Minista Ahmed tana cewa, “za a yi amfani da kudaden wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya tare da bai wa jihohi tallafi,” domin yaki da cutar ta coronavirus.
A nasa bangaren, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal ya ce bukatar neman kudaden na da matukar muhimmanci saboda kasar na cikin yanayi na gaggawa a wannan lokaci.
Facebook Forum