Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Na Sake Kara Yaduwa a Turai - WHO


Hukumar Lafiya Ta Duniya - WHO
Hukumar Lafiya Ta Duniya - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya - WHO, ta yi kashedi jiya Alhamis cewa annobar coronavirus ta soma sake yaduwa a fadin nahiyar Turai a cikin wani mummunan yanayi, kana wata matashiya ce da ya kamata ta zaburad da gwamnatocin kasashen Turai.

Shugaban hukumar ta WHO a Turai Dr. Hans Klug ya fada a yayin taron manema labarai ta yanar gizo daga birnin Copenhagen cewa, cutar tafi yaduwa cikin gaggawa tsakanin ‘yan shekaru 25 zuwa 49.

WHO ta kuma ce cutar na kara ta’azzara tsakanin tsofaffi.

Kluge ya ce karuwar adadin kamuwa da cutar na nuni da karuwar gwaje-gwajen da ake yi, amma kuma hakan na nuna mummunan yanayin yaduwar cutar a duk fadin yankin.

Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus

Kluge ya gargadi kasashen Turai akan takaita ranakun killace masu cutar, kana ya yi kira gare su da su dauki kwararan matakai na shawo kan yaduwar cutar, wadda ya ce tana da hatsarin gaske a duk lokacin da aka sanya siyasa a lamarin ta, ko kuma aka ki fadawa jama’a gaskiya.

Ya ce “inda cutar za ta tafi daga nan yana hannunmu, mun yi yaki da ita a can baya, a yanzu ma muna iya ci gaba da yakar ta.”

A nan Amurka kuma, alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fitar a wannan mako, sun nuna cewa yara ‘yan kasa da shekaru 21 a cikin tsirarun jinsin Amurka ne suka fi kamuwa da COVID-19, idan aka kwatanta da masu irin wadannan shekaru a cikin farar fatar Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG