Faduwar farashin man fetur sakamakon tsayawar harkokin tattalin arziki a kasashen duniya dake da nasaba da annobar cutar coronavirus ya sa ana saida man fetur na kasar Amurka kasa da dala biyu, yayin da a wasu kasashen bai haura dala goma ba.
Kasashen duniya da masana harkokin tattalin arziki na bayyana damuwa akan karyewar farashen da kuma yanayin tattalin arzikin duniya.
Dakta Dauda Muhammad Kontagora, masanin harkokin tattalin arziki a Najeriya, ya ce kasuwar man ta cunkushe ne saboda babu masu saye sakamakon matakan da kasashen duniya suka dauka na rufe duk wasu harkokin kasuwanci da kuma saka dokokin hana zirga-zirga don dakile yaduwar cutar coronavirus.
Kasashen da suka ci gaba, musamman China dake kere-kere da dangantakar kasuwanci mai karfi, tana daya daga cikin kasashen dake bukatar mai saboda injinan da take amfani da su, amma yanzu komai ya tsaya. Wannan na daga cikin dalilan da suka haddasa faduwar farashen.
Hakazalika rufe harkokin kasuwanci da hana zirga-zirga a kasashe sun kawo tangarda ga tattalin arzikin kasashen duniya, a cewar Muhammad, shi ya sa wasu kasashen ke yin kira ga mahukuntansu da su sake nazarin matakan da suka dauka ko su bullo da wata dabarar.
Najeriya na daga cikin kasashen da suka dogara ga man fetur don samun kudaden shiga. Dakta Muhammad ya ce duk da cewa kasar ta zaftare kasafin kudinta na bana a baya, matakan hana zirga-zirga a kasar yanzu sun kara zafafa lamarin.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum