Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: IMF Ta Bukaci Gwamnatocin Gabas Ta Tsakiya Su Dauki Matakan Gaggawa


IMF
IMF

Hukumar bada lamuni ta duniya da ake kira IMF a takaice ta yi kira ga gwamnatoci a Gabas ta tsakiya da su dauki matakan gaggawa na tunkarar yiwuwar faduwar tattalin arziki sakamakon barkewar annobar cutar coronavirus.

Daraktan hukumar IMF a yankin Gabas ta tsakiya da Tsakiyar Asiya, Jihad Azour, ya fada a cikin wani rahoto a yau Talata cewa yaduwar cutar ya zama wani babban kalubale a yankin.

Azour ya kuma ce yadda annobar cutar coronavirus wato covid-19 ke yaduwa cikin sauri, da kuma faduwar darajar danyan mai saboda rikicin farashin tsakanin Saudi Arabia da Rasha, ka iya kawo babban cikas ga lamurran tattalin arziki a yankin, musamman a harkokin yawon bude ido, kana kuma ya kara adadin wadanda basu da aikin yi.

Hukumar IMF ta ce kasashen da yaki ya daidaita kamar Iraqi da Sudan da kuma Yemen su ne suka fi fuskantar hadarin cutar annobar coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG