Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadi kan karuwar adadin masu coronavirus a kasashen da ke fama da talauci.
A wani taron manema labarai wanda hukumar ta WHO kan yi dangane da cutar, Shugaban hukumar ya ce, "Hankalinmu a tashe yake, saboda karuwar masu coronavirus a kasashe masu karanci da kuma masu tsaka-tsakin karfin tattalin arziki."
WHO ta ce a cikin sa’o’i 24 cutar ta kama mutum 106,000, wato adadi mafi yawa a cikin kwana daya tunda cutar ta barke a karshen shekararr da ta gabata.
Tedros ya ce WHO za ta ci gaba da taimaka wa kasashe domin tabbatar cewa sun samu kayakin kariya da zasu bai wa jami’an lafiya da kuma majinyata saboda a tabbatar cewa fannin kiwon lafiya bai fuskanci wani kalubale ba.
Facebook Forum