Duk da rashin tabbas da farashin hannayen jari ke fuskanta sanadiyyar cutar Coronavirus, an rufe kasuwanin inda farashinsu suka dan farfado, lamarin da ya sa aka rufe dan gibin asarar da aka tafka a baya, sannan hakan ya karawa masu saka hannayen jari kwarin gwiwa.
A nan Amurka alkaluman manyan Kamfanoni sun tashi yayin da aka rufe kasuwar a ranar Alhamis.
Kasuwar Dow Jones ta tashi da maki 33 ko kashi sufuli da dugo 14, abin da ya sa ta doshi kusan maki 23,537.
S&P kuwa ta tashi da kusan maki 16 ko kashi sufuli da dugo 55 inda ta tashi da kusan maki 2,799.
Kasuwar Nasdaq ta tashi da maki 139 ko kashi 1.66 inda hakan ya ba ta damar dosar kusan maki 8,532.
Hakazalika kasuwannin a nahiyar turai ma sun farfado a ranar ta Alhamis, inda Kasuwar FTSE a London ta tashi da maki sufuri da dugo da 55.
Haka ma kasuwar DAX a Frankfurt a kasar Jamus ta tashi da maki sufuli da dugo da 21.
Sai dai kasuwar CAC-40 a birnin Paris da ke Faransa ta fadi da warwas.
Facebook Forum