Gidauniyar Aliko Dangote ta ba da gudunmawar cibiyar gwaji ta tafi da gidanka domin gano masu dauke da kwayar cutar Coronavirus a Kano.
A ranar Lahadi ne jami’an gidauniyar suka mika kayayyakin cibiyar ga kwamitin yaki da cutar na jihar Kano wadda za ta rika gwada mutane 400 a kowace rana.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da adadin wadanda suka kamu da wannan cutar ta COVID-19 ke ci gaba da karuwa a jihar Kano, baya ga matsalolin karancin kayayyakin aiki ga ma’aikatan lafiya.
Daraktar gidauniyar Dangote, Hajiya Zuwaira Yusuf ta fayyace hikimar wannan hubbasa daga attajirin ga Kano.
"Gidauniyar mu ta dauki nauyin dukkanin gwaje-gwajen da za a yi da kuma kudaden da za a biya masu aikin wurin da duk wani kayan kare kai da ake bukata."
A nasa bangaren, Dr. Sani Gwarzo, shugaban kwamitin tarayya na musamman kan yaki da cutar Corona a jihar Kano ya ce babu ko shakka wannan yunkurin na gidauniyar Dangote ya zo akan gaba.
Ya ce "zuwan wannan yunkurin ya zo mana a lokacin da jihar mu ke bukatar wannan, amma duk da hakan ba zai isa ba."
Ya zuwa yanzu mutum 342 ne cutar ta harba a jihar ta Kano.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum