Kungiyar kasashen Turai ta EU ta ware zunzurutun kudi dala biliyan 580, don rage radadin da annobar coronavirus ta janyo a kasashen dake cikin kungiyar.
Shugaban kungiyar Charles Michel ya bayyana a jiya Alhamis cewa, za a fara raba wadannan kudaden ne daga ranar daya ga watan Yuli. Michel ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen bai wa jama’a tallafi, da kuma tallafa wa kamfanoni, da kara inganta tsarin kiwon lafiyar kasashen.
Ya kuma ce “mun cimma matsaya daya, game da cewa, lafiya da halin da jama’a suke ciki shine kan gaba, kana zamu ci gaba da bibiyar halin da ake ciki musamman a yanzu da muke tunkarar lokutan shagulgula, zamu dauki matakai da suka dace da kuma sassauta dokar takaita zirga-zirga.”
A taron da suka gudanar jiya Alhamis ta kafar yanar gizo, shugabanin kungiyar EU, sun amince da bada wadannan kudaden na tallafi, amma basu fadi adadin wadanda zasu ci gajiyar kudaden ba cikin kasashe 27 na kungiyar. Bugu da kari hukumomin sun ce dala tiriliyan daya da miliyan 100 daya zuwa dala tiriliyan daya da miliyan 600 ake bukata.
Shugabar kwamitin kungiyar ta EU Ursula Von der Leyen, ta ce tasirin da tattalin arziki ya samu a sanadiyyar wannan annobar ta COVID-19 ba karamin matsi bane a wannan zamani.
Facebook Forum