Babban Bankin Najeriya CBN, ya sanar da ware Naira biliyan 50 na tallafi wanda zai ragewa alummar kasar raddadi da kuma asarar da suka tafka a sakamakon cutar Coronavirus.
Bankin a karkashin jagorancin Godwin Emefiele ya ce, wadanda za su ci gajiyar tallafin za su kasance magidanta ne da suke gudanar da wasu sana'o'i wanda suka samu koma baya a sakamakon cigaba da yaduwar Coronavirus.
Hakazalika, masu masana'antu da suke da hujjoji kwarara da suka hana su ci gaba da kasuwancin su a sanadiyar hana fita su ma zasu samu tallafin.
Daya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan Arewa, Nastura Ashir Sheriff ya ce bai gamsu da yadda za a rarraba wadanan kudade ba.
Ya kuma bayar da shawarar cewa a kasa kudin kashi 37 wato a ba jihohi 36 har da birnin tarayya Abuja sai su raba abinsu domin su ne suka san wadanda za a ba kudin a jihohin su.
Shi kuwa dan Majalisar wakilai a jihar Nasarawa Abdulmumuni Mohammed Ari da ya ce, lallai ya yarda da tsarin rabon jiha jiha, amma yana so a kullum aka fitar da irin wanan kaso, yana kira ga yan Arewa da su nemi cika ka'i'dojin domin su ma su samu tallafin.
Saurarri wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum