Alkaluman da aka fitar a hukumance kan adadin wadanda suka rasa ayyukansu a Amurka sanadiyyar cutar coronavirus ya kai kashi 14.7 cikin 100.
Manyan jami'an Fadar White House sun yi hasashen cewa adadin zai iya kai wa kashi 25 cikin 100 kafin tattalin arzikin kasar wanda ya fi kowanne karfi a duniya ya fara farfado wa.
Sakataren baitul malin kasar, Steven Mnuchin ya fadawa gidan talbijin na Fox News a ranar Lahadi cewa, "akwai yiwuwar adadin ya karu sannan daga bisani ya farfado cikin wannan shekara zuwa badi."
Ya kara da cewa adadin marasa aikin yi zai iya kai wa kashi 25 cikin 100, yayin da mai ba da shawara kan tattalin arziki a Fadar White House, Kevin Hassett ya fada wa shirin “Face The Nation” na gidan talbijin din CBS cewa yana tsammanin adadin zai tsaya a kashi a 20 cikin 100, yayin da cikin watannin Mayu da Yuni, wasu miliyoyin mutane da suka rasa ayyukansu za su mika koken neman tallafi.
Shi dai wannan adadi na 14.7 cikin 100 da aka fitar a ranar Juma’a, shi ne mafi muni da Amurka ta taba gani tun bayan gagarumin karayar tattalin arzikin da ya faru cikin 1930s.
Amma Mnuchin ya ce "ba laifin ma'aikata ko wuraren kasuwancin Amurka ba ne."
Facebook Forum