Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus Ta Halaka Dan Shekara Shida a Kenya


Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta

Wani yaro dan shekara shida ya rasu sanadiyyar cutar coronavirus a Kenya.

Ma’aikatar lafiyar kasar ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a inda ta ce yaron shi ne mafi karancin shekaru da ya mutu sanadiyyar cutar a kasar.

“Ina mai bakin cikin sanar da ku cewa, mun rasa wani mara lafiya sanadiyyar cutar coronavirus, ba wani ba ne illa wani yaro dan shekara shida da ke fama da wasu cututtuka.” In ji Mercy Mwangagi, babbar sakatariya a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta Kenya.

“Yanzu adadin wadanda suka mutu sanadiyyar wannan cuta ya kai mutum hudu.” Ta kara da cewa.

Yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar ta COVID-19 a Kenya ya kai 122.

A ranar Alhamis ma’aikatar lafiyar ta ce sabbin mutanen da suka kamu da cutar ba daga kasashen wajen suka shigo ba tana mai cewa daga cikin gida cutar ta yadu.

A makon da ya gabata gwamantin Kenya ta sanya dokar hana fita tsakanin karfe 7 na yamma zuwa 5 na safe, baya ga wasu matakai da ta dauka a kokarin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG