Mayar da hankali akan matakan rigakafin cutar shine daya-dayar makamin da ya rage wa kasashe masu tasowa irinsu Nijer domin kare kai daga anobar cutar coronavirus inji shugaba Issouhou Mahamadou ganin yadda abin ke kokarin zama gagara badau ga kasashen da suka mallaki manyan asibitoci da kwararrun likitoci, mafari kenan na daukar matakan rufe iyakokin sama da na kasa, da makarantun boko, gidajen cin abinci, da na shan barasa, da dai sauransu.
A ra’ayin wani dan Nijer Ibrahim Kantama, gwamnatin ta sara akan gaba, saboda a cewar sa, ko addini ya yarda a dauki wannan matakin idan aka sami bullar annoba.
Matakin gwamnatin ta Nijer ya haramta taron mutanen da yawansu ya zarta 50 kuma abin zai shafi bukukuwan suna, da aure da makamantansu. A cewar shugabar kungiyar matasa ta JENOM Falmata Daya, akwai alamar wuce makadi da rawa wajen bullo da wannan tsari saboda a ganinta zai yi wuya a kiyaye matakin.
A ranar 20 ga watan nan na Maris ne matakin rufe iyakokin Nijer zai soma aiki to amma a ganin shugaban kungiyar muryar talaka Nassirou Seidou, irin wannan jinkiri ba zai haifar wa kasa da mai ido ba.
A jawabinsa na jiya Talata da dare, shugaba Issouhou Mahamadou ya tabbatar da cewa ba a samu bular wannan cuta a Nijer ba a lokacin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum