Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Corona: Mai Yiwuwa A Dawo Da Tsauraran Matakai A Najeriya


Wasu magungunan rage radadin corona da aka kawo Najeriya
Wasu magungunan rage radadin corona da aka kawo Najeriya

Ganin yadda cutar corona ke barazanar sake dawowa gadan gadan musamman a sassan duniya, hukumomi a Najeriya sun shiga yin gargadi ga jama'a game da bukatar cigaba da daukar matakan kandagarki irinsu bayar da tazara da sanya takunkumin kariya.

Gwamnatin Najeriya ta gargadi al’ummar kasar da suyi taka tsan tsan wajen kauce wa kamuwa da cutar corona, inda take cewa rashin daukar matakai da suka dace ka iya sanya a sake killace jama’a cikin gidajensu, a kuma daidai lokacin da kungiyar hadakar ma’aikatan lafiya ta kasar ke barazanar daukar mataki idan har Gwamnatin ta kasa cika musu alkawuransu.

Sakataren gwamnatin kasar, Boss Mustapha ne ya sanar da haka, sakamakon ganin yadda cutar ke sake dawowa a kasashen da suka yi nasarar dakile ta, abinda ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya ke dada gargadi ga jama’a akan bin matakan kariya, hakazalika hukumar takaita yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ta ce ta na aiki tare da hadin gwiwar cibiyar nazarin lafiya ta Najeriya da takwarorinsu kan gudanar da binciken fadada sanin wadanda ke dauke da cutar a kasar.

Tsohon shugaban hukumar ta NCDC, Farfesa Abdulsalam Nasidi ya yi tsokaci kan muhimmancin wadannan matakai da kuma halin da ake ciki.

A daya bangaren kuwa bayan Kungiyar hadaka ta ma’aikatan lafiya a Najeriya, JOHESU ta dawo daga yajin aikin da ta shiga na mako guda a ranar Litinin din nan, saboda abin da ta kira rashin biyan hakkokinta da gwamnatin kasar ta yi, ya zama na baya bayan nan a matsalolin bangaren lafiyar kasar, inda a yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura dubu 57. Kuma akwai yiwuwar kungiyar ta sake komawa yajin aikin a cewar shugaban kungiyar rashen jihar Kano Dakta Murtala Isa Umar.

Dan Majalisar Wakilan Tarayya kuma shugaban kwamitin kiwon lafiya, Dakta Yusuf Tanko Sununu, ya bayyana cewa gwamanti na iya kokarinta wajen samar da mafita.

Ga cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim ta sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG