Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya: Ana Zargin Gwamnatin Kano Da Cefanar Da Filin Gidan Zakkah, Janairu 11, 2021


Sarfilu Hashim Gumel
Sarfilu Hashim Gumel

Filin Ciki Da Gaskiya ya fara duba batun korafin jama'a a Kanon dabo, kan yunkurin gwamnatin jihar na raba wasu filaye ko wurare masu muhimmanci ga daidaikun mutane da wasu ke ganin hakan bai dace ba ko ya sabawa doka.

Daya daga cikin wuraren da ake zargin gwamnatin jihar Kano da cefanarwa shine filin gidan zakka da ke Goron Dutse cikin badala a tsohon birnin Kano.

Majalisar kula da gidan zakkar ta ce an samu gidan tun zamanin tsohon gwamnan jihar marigayi Abubakar Rimi, inda a ka gina shi a matsayin wakafi ko aikin samun lada ta hanyar amfani da ginin wajen tara zakka da rabawa mabukata.

Majalisar ta ce gwamnati ta yanka harabar gidan zakkah ga wasu mutane don gina shagunan kasuwa.

Saurari shirin Ciki Da Gaskiya:

Ciki Da Gaskiya: Ana Zargin Gwamnatin Kano Da Fansar Da Filin Gidan Zakkah - 12'46"
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:46 0:00


XS
SM
MD
LG