Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce zazzabin cizon sauro, ko maleriya, shine babban abinda ke kashe yara 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa a nahiyar Afirka, inda yara uku suke mutuwa cikin kowadanne mintoci biyu.
Hukumar ta ce a kowace shekara, mutane akalla miliyan daya suke mutuwa a sanadin zazzabin cizon sauro, kashi 90 daga cikin 100 kuwa suna mutuwa ne a nahiyar Afirka.
Wannan kashedi na hukumar, an gabatar da shi jiya alhamis, ranar da aka yi gangamin yaki da cutar a duk fadin nahiyar Afirka, domin wayar da kan jama'a game da wannan cuta da sauro ke yadawa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yankin kudu da hamadar Sahara a nahiyar Afirka, nan ne ake da wani irin jinsin sauro wanda ya fi kowanne a duniya kuzarin yada wannan cuta ta Maleriya.
Hukumar ta ce yanzu babbar matsalar da kasashen Afirka suke fuskanta ita ce ta yadda kwayoyin cutar Maleriya suka fara jurewa maganin "Chloroquine", magani mafi arha, kuma wanda aka fi yin amfani da shi wajen yakar cutar maleriya.