Irin wannan korafi ne ya sa shugaban Cibiyar Kare Hakkin Masu Amfani da wutan lantarki a Najeriya, wato Nigeria Consumer Protection Network a turanci, Kola Olubiyo, ya gana da manema labarai a Abujan, inda ya nuna cewa an kwashi tsawon lokaci ana fama da rashin wuta a kasar, bayan an dauki matakai da dama, na gyara al'amarin.
Olubiyo ya ce cibiyar da ya ke shugabanta, ta rubuta wa Shugaban Kasa wata takarda ta musamman, akan yadda ake fama da rashin wutan lantarki, domin akwai abin dubawa a harkar sayar da hannun jarin, baki daya
Shikuwa, tsohon shugaban Ma'áikatar Wuta ta Kaduna, Idris Mohammed Madakin Jen, ya ce gwamnatin tarayya ta san irin matakin da za ta dauka a irin wannan yanayin
Amma mai ba shugaban kasa shawara a harkar manyan ayyuka, Ahmed Zakari Santurakin Kazaure ya ce gwamnati tana aiki tukuru wajen magance matsalar.
Abin jira a gani shi ne irin matakin da mahukunta zasu dauka domin biya wa masu amfani da wutan latarki bukatun su na yau da kullum saboda tallafawa kananan sana'o'in hannu wajen farfado da tattalin arzikin su.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: